Sheikh Lawal Kaura Zaria

Sheikh Lawal Kaura Zaria

Karatu

Ba Karatu

TARIHIN SHEIKH LAWAL KAURA (Masanin sirar annabi s.a.w) . #Sunansa: Muhammad Auwal Ibrahim Kaura Zaria. Mahaifinsa babban malami ne a lokacin sarki Jafaru ishaq yayi mufty na alkali(mai bada fatawa) na kotu. An haifi shehin malamin ne a karamar hukumar makarfi a sakamakon aiki da yakai mahaifinsa garin daga Zaria, kimanin 1950. . Sunan mahaifiyarsa Hajiya Rabi'atu(labuje/goggon amaru) wacce shahararriyar ce wajen kasuwanci da rufin asiri na dukiya da Allah yayi mata, har yanzu akwai gidah na musamman da ake kiransa da sunanta a Unguwar Amaru dake birnin Zaria(gidan labuje). Shehin malamin ya bada gudumowa matuka wurin yada addinin Allah da bada karatu wanda mutafannini ne. #karatun sa: shehin malamin ya fara karatu a hanun mahaifinsa Mal. Ibrahim mufty gami da karatun allo hanun mal. Umar kawun makaranta. Sannan ya zarce karatunsa na boko a firamare ta sarki Jafaru isyaku L.G.A dake kusafa zaria. . Malamin ya bazama wurin neman ilimi hanun malamai daban-daban, # daga malamansa sun hada da: -Sheikh Muhammad mitwalla El-sha'arawy dake qasar masr(Egypt). -Malam Jibril (Malam na'iya Zaria) wanda shehin na cikin manyan almajiransa wanda sukayi Jan-baki a zaure tun yana karami a cikinsu saboda hazaka. -Malam Ibrahim(Bala Sufi,mai ashafa). -Malam ishaka nagusau. Shehin ya fara bada karatu a zauren mahaifinsa a gabansa tun yana da rai. Haka ya cigaba da bada karatu ga al-umar musulmi babu dare ba rana daga kowwace nahiya ta kasar nan harma da wajenta. # kadan daga almajiransa: -Sheikh Nasidi Abubakar gwauron-dutse Kano. -Alkalin alkalai Mal.Maccido Ibrahim (grand khadi). Wanda aminin malamin ne don ranah daya ma aka haifesu. -Maigirma sarkin birnin gwari Alh. Zubairu Jibrin mai-gwari. Shima amininsa ne tun yanada sarautar madakin birnin gwari. -Sheikh Malam sabitu Sardauna kusfa wanda shima amininsa ne. -Sheikh Mal.Abidurrahman kusfa Zaria. -Malam Muhammad bagudo. Da sauransu wanda basu kidanyuwa. Wanda Allah ya azurta shi da baya Nagari wanda dukkansu malamai ne suna bada karatu ta kowwace nahiya. Shehin malamin ya ziyarci dakin Allah sau 86, Hajji 34 umarah 52 wanda Allah ya azurta shi da shiga har cikin dakin ka'aba ma a lokacin Shagari. . Shehin ya bada gudumowa na gina masallatai,makaratun ilimi, islamiyyah da boko, zauruka harma da kasuwanni da masana'anta ta Alqana'ah. Allah ya azurta shi da 'ya'ya da ya bari 30 da jikoki 36 wanda mafi yawancinsu malamai ne kuma mahaddata Al-qur'ani. Allah ya karbi ransa a shekara ta 2014 wanda yayi dai-dai da lahadi 12 ga watan Ramadan 1434, wanda akayi janazarsa da ba'a taba yin irinsa ba a garin zaria saboda Jama'a, tun bayan rasuwar Malaminsa Malam na'iya. Ya bar duniya yanada kimanin shekaru 63. Allah yayi masa rahma ya bamu albarkacin su da kyakkyawar karshe.